Mummunan bayanin da ke fitowa daga Jihar Neja ya tabbatar da kisan a?alla sojoji 30, yan sandan mobal 7 da kuma farar hula da dama, a wani ?azamin farmaki da mahara su ka kai wani wurin ha?ar maadinai da ke cikin ?aramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da cewa an kai mummunan harin, kuma ta ?ara da cewa har yanzu ba ma tabbatar da ko adadin yawan wa?anda aka kashe ?in ba.
Mazauna yankin da aka kai farmakin sun tabbatar da cewa sune wa?anda su ka fita tsintar gawarwaki baya ?ura ta lafa, sun ?auko gawarwakin sojoji 30 da kuma da mobal 7 a cikin dajin da ke kewaye da wurin ha?ar maadinan a safiyar Alhamis.
Haka kuma an tabbatar da kwaso gawarwakin fararen hula shida a cikin daji.
Mazauna yankin sun ?ara da cewa maharan sun kwashi mutane da dama ciki har da yan Chana, su ka arce da su a ranar Laraba.
Wani jagoran matasa a Shiroro mai suna Yusuf Kokki, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mazauna yankin sun gani kuma sun ji lokacin da maharan ke wa wurin ha?ar maadinan zabarin ruwan wuta da muggan makamai.
A yanzu haka a kowane lokaci yawan wa?anda aka kashe a harin wanda aka kai Ajata-Aboki sai ?aruwa ya ke yi. Domin zaman yanzu dai iyar gawarwakin da aka tsinto har da na sojoji 30 ne.
Kokki ya ce ana sa ran ?ara gano wasu gawarwakin, saboda har zuwa safiyar ranar Alhamis masu ceto na ci gaba da neman gawarwaki a cikin jeji.
Ya ce maharan sun dira wurin ha?ar maadinan, wadda mallakar wasu yan Chana ce, inda su ka bu?e wa maaikata da masu tsaro wuta.
Ya ce tun a wurin ha?ar maadinan take aka bindige mobal 7, da farar hula 6.
Sojojin da aka girke a garin Erena su ka garzaya wurin domin kai ?aukin gaggawa, inda ba su ankara sai mahara su ka afka masu da harbi, inda aka bindige sojojin Najeriya da dama.
Da yawan wa?anda aka ji wa ciwo kuma an garzaya da su asibiti domin kula da su.
Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Neja, Emmanual Umar, ya ce artabun da aka yi da sojoji ya sa sojojin sun ceto jamaa da dama da hannun mahara.

