Labarin dake shigo mana daga Minna babban birnin jihar Neja na bayyana cewar Kamfanin Abuja Electricity Distribution Company watau AEDC masu raba wutar lantarki a jihar sun datse wutar gidan Gwamnati da maaikatun gwamnati.
Hakan ya biyo bayan tulin bashi da kamfanin na AEDC yake bin gidan gwamnati, maaikatu da hukumomin jihar ta Neja. AEDC sun ba gwamnatin Neja waadi ta biya kudin, da abin ya gagara sai aka yanke masu wuta.
Kamar yadda jamiin hulda da jamaa na kamfanin AEDC, Mohammed Pele ya shaidawa ‘yan jarida a ranar Jumaa, kudin da suke bi ya kai N1.3bn.
Mohammed Pele yace baya ga maaikatun gwamnatin Neja, kamfanin ya yanke wutar lantarki a gidan gwamnati da asibitin da ke fadar gwamna.
Pele yace kwanakin baya majalisar dokokin Neja ta sa baki a maganar bashin, har aka amince gwamnati za ta biya kamfanin 80% na kudin da suke bi.
Tun da aka yi wannan magana da yan majalisar jihar, jamiin yada labarai na kamfanin yace gwamnatin Neja ba ta biya su ba, wanda hakan ya sanya dole aka datse su.

