Labarin dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar rundunar Sojan Sama ta ?asa ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe tarin ‘yan bindiga a Jihar Neja.
Sanawar da rundunar ta fitar ta ce a ranakun karshen makon nan ta kai harin a kan Aminu Duniya lokacin da yake jagorantar wani taro da mayakan kungiyar a garin Kurebe na Karamar Hulkumar Shiroro.
“Sai dai babu tabbas ko shi ma Aminu Duniya ya mutu a harin,” a cewar sanarwar.
“Yayin da sojojin kasa suka toshe hanyoyin yankin, jirgin sojin sama ya bude wuta a inda ‘yan ta’addan suke kuma an tabbatar da mutuwar ‘yan ta’addan masu yawa.”

