Labarin dake shigo mana daga Mina babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar rundunar ‘yan sandan jihar ta yi nasarar damke wani hatsabibin matashi mai shekaru 26 mai suna Umar Mohammed wanda aka fi sani da Babuga Yellow, kan zargin sata da garkuwa da mutane.
A wata takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, yasa hannu a ranar Juma’a a Minna, wanda ake zargin ya bayyana cewa tawagarsa ta shirya aikata mummunan aiki kafin a kama shi.
“Ya bayyana cewa, miyagun sun shirya sace wasu fitattun mutane biyu a kauyen Garatu,” takardar tace. wanda ake zargin ya kara da bayyana sunayen abokan aikinsa wadanda har yanzu ba a kama su ba, inda ya kara da cewa suna da hannu wurin garkuwa da mutane tare da karbar kudin fansa da kuma satar shanu.
“A yayin tuhuma, ya sanar da cewa ya na cikin kungiyar ‘yan bindiga wadanda suka kware da satar shanu tare da satar mutane domin karbar kudin fansa. Ya bayyana sunanyen ‘yan kungiyarsu kamar haka: Bokolore, Ruwance, da Giware wadanda yanzu haka basu shigo hannu ba.
“Bayan jerin bincike, ya bayyana cewa sun dinga satar shanu a wurare daban-daban da suka hada da Beji, Wushishi da Kataeregi.”

