Site icon Muryar 'Yanci

Nasarar Uba Sani Nasara Ce Ga Jama’ar Kaduna – Shehu Molash

An bayyana nasarar da za?a??en Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC ya samu a za?en da ya gabata a matsayin wata nasara ce ga jama’ar jihar gaba ?aya.

Mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Kaduna kan harkokin siyasa Alhaji Muhammad Shehu Molash ya bayyana hakan a sakon godiya da ya aike wa jama’ar Jihar Kaduna kan nasarar sabon Gwamna Malam Uba Sani.

Molash wanda shine mai magana da yawun kwamitin ya?in neman za?en Shugaban ?asa na jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso yamma, kuma mataimakin darakta na tsare-tsare da harkar ya?a labarai na kwamitin ya?in neman za?en gwamnan jihar Kaduna a Jam’iyyar APC, yace jama’ar Jihar za su dara da irin salon shugabancin Sanata Uba Sani.

Molash ya godewa dukkanin jama’ar Jihar Kaduna bisa ga za?en da suka yi musu, inda ya tabbatar ba su yi za?en tumun dare, domin za su ga aiki babu kama hannun yaro domin Malam ne ya tafi kuma Malam ne ya dawo.

Exit mobile version