Site icon Muryar 'Yanci

Najeriya Za Ta Haramta Kiwon Dabbobi A Sarari

Dokar ta tsallake karatu na biyun ne bayan da shugaban majalisar Godswill Akpabio ya bu?aci ‘yan majalisar da su ka?a kuri’ar amincewa ko kin amincewa, nan take kuma adadi mafi yawa suka amince da haramta kiwo a sararin.

Bayan kammala ka?a kuri’ar majalisar ta bu?aci kwamitocinta kan harkokin noma, kasuwanci da zuba jari da kuma shari’a da su sake bibiyar dokar tare da dawo da ita majalisar don ?ar?arewa.

Wa’adin wata guda ne aka baiwa kwamitocin don su kammala wannan aiki da aka basu mai cike da sarkakiya a Najeriya.

Wannan doka dai idan har ta tabbata, zata haramtawa duk wani makiyayi yawo da dabbobinsa, a sassan ?asar don kaucewa matsalolin da ake samu musamman tsakanin manoma da makiyaya da kuma harkokin tsaro da ke ?ara ta’azzara yanzu haka a ?asar.

Najeriya ta jima tana fama da matsalolin rikici tsakanin makiyaya da manoma, lamarin da ke haifar da ?azamin rikicin da kan yi sanadiyyar rasa rayuka.

Bayanai sun ce a?alla mutane miliyan 5 ne suka tsere daga muhallansu a dalilin rikicin makiyaya da manoma, yayin da ake tafka asarar akalla dala miliyan 3 da rabi kowacce shekara sanadin wannan rikici

Exit mobile version