Site icon Muryar 'Yanci

Najeriya Ta Samu Shiga Gasar Nahiyar Afirka

Super Eagles

Najeriya ta samu gurbin shiga gasar Kofin Afirka ta 2021 bayan Lesotho da Sierra Leone sun buga canjaras a wasansu a rukunin L.

Sakamakon wasan ne ya bai wa tawagar ta Super Eagles damar shiga gasar tun kafin take wasanta da Benin a yau Asabar.

Najeriya ta doke Benin 0-1 a wasan da suka take da ?arfe 5:00, abin da ya sa ta samu maki 11, Benin na da bakwai, Sierra Leone na da hu?u sai kuma Lesotho mai uku a rukunin.

?asashen da suka ?are a mataki na ?aya da na biyu ne za su halarci gasar a Kamaru, wadda ?asashe guda 24 za su fafata a karo na 33.

Benin da Najeriya ne suka samu gurbin shiga gasar daga rukunin na L.

Tawagar Super Eagles ta lashe kofin gasar sau uku a tarihi.

Sauran ?asashen da suka fito zuwa yanzu:

Exit mobile version