An bayyana cewar Najeriya ta shiga cikin wani yanayi da matsayi mafi muni a tarihi karkashin shugabancin Shugaban ?asa Buhari, inda ya komai yake tsaya cak kowa na cikin rudani.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin tsohon ?an takarar shugabancin kasa kuma shugaban Jam’iyyar adawa ta ADP Injiniya Yagbagi Yusuf Sani a tattaunawa da gidan talabijin na Liberty yayi dashi cikin shirin “State Of The Union” a karshen mako.
?an siyasar ya kara da cewar harkar tsaro ta yi lalacewar da bata taba yi ba a baya tattalin arziki ya fa?i warwas ga matsalar rashin aiki a tsakanin Matasa lamarin da ya taimaka wajen hauhawar rashin tsaro a kasar.
Injiniya Yagbagi ya cigaba da cewar halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu ya wuce Min Sharrin ya kai Ma Halaka, sakamakon yadda harkar ilimi ke fuskantar barazana daga hannun ‘Yan Bindigar Arewa masu kisa da yin garkuwa da mutane, lamarin da ya sanya makarantu da dama suke kulle a yankin Arewacin kasar.
“Jagoranci a Najeriya ya yi muguwar lalacewa ta dukkanin matakai ‘yan Najeriya na rayuwa ne a wani yanayi irin na wa?anda yaki ya ?ai?aita su a kasar su”.
Wani ?arin abin takaici kuma shine yadda a har kullum talauci ke ?ara ?amari a ?asar, masana’antu sun kasance a kulle, da yawansu sun yi ?aura zuwa ?asashe ma?wabta saboda halin da Najeriya ke ciki.
Injiniya Yagbagi ya bayyana cewar Najeriya babbar kasa ce da ke bu?atar a samu jajirtaccen Shugaba wanda zai jagoranci ?asar ya kai ta tudun mun tsira, abin da kuma kasar ta rasa kenan Buhari ya gaza matuka ana rayuwa a Najeriya tamkar babu shugaba ne, saboda haka ‘yan Najeriya su shiga hankalinsu domin sanin wanda za su zaba a za?ukan dake tafe, inji shi.

