A cewar rahoton bincike da ake yi gameda ayyukan taaddanci da aka fitar a wannan shekarar, ya nuna cewar ayyukan taaddanci a karon farko sun ragu sosai a kasar tun bayan shekarar 2011.
Daga tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020, Najeriya na mataki na hudu a jerin kasashen da aka fi samun taaddanci a duniya, duk da cewa lamarin ya fi kamari a shekarar 2016 da 2015 da kasar ke a mataki na 2.
Kungiyoyin masu ta da kayar baya irin su Boko Haram da kuma ISWAP sun yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a shiyar Arewa maso Gabashin kasar, a hare-haren da suke kaiwa.
A cewar rahoton, a shekarar 2021 mutane 497 suka mutu sanadiyar ayyukan taaddanci inda kuma adadin ya ragu zuwa 385 a shekarar da ta gabata.
Haka nan kuma, adadin hare-haren taaddancin da aka kai a shakarar 2021 ya ragu zuwa 214 sannan a shekarar da ta gabata ya kara yin kasa zuwa 120, wanda shine karo na farko da aka samu irin wannan raguwa tun shekarar 2011.

