Labarin da ke shigo mana daga Jihar katsina na bayyana cewar Tsohon Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga ya bayyana cewa abubuwa na ci gaba da tabarbarewa a Najeriya duk da adduoin da alummar kasar ke yi a kullun saboda kasar na karkashin laantar Ubangiji.
Farfesa Lugga ya ce hakan ya faru ne sakamakon rashin shugabanci nagari, yana mai jan ayoyi daga Al’kur’ani mai girma da littafi Bibul.
Wazirin Katsina na biyar ya yi wannan martanin ne a gidansa yayin da yake zantawa da manema labarai a daren ranar Jumaa jajibirin Sallah.
Farfesa Lugga ya shawarci sarakuna da shugabannin addinai wadanda ke tsoron bayar da shawarwari na gaskiya ga shugabannin siyasa da su yi murabus ko kuma a tsige su don ba wadanda za su iya aikin yadda ya kamata dama.
Yanzu haka, muna a cikin tsarkakken lokaci inda Musulman Najeriya ke a Makka don aikin Hajji sannan Kiristocin Najeriya na a Jerusalem suna gudanar da aikin Hajjin Ista.
Gwamnatin tarayya ta ayyana hutun Sallah, inda ta bukaci Musulmai da su yi adduan zaman lafiya tsaro da ci gaban Najeriya.
Majalisar harkokin Musulunci da duk sauran kungiyoyin Musulunci sun bukaci ayi addua. Kungiyar Kiristocin Najeriya da sauran kungiyoyin kiristanci sun yi kira ga adduoi. shugaban kasa, gwamnoni, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai sun yi kira ga adduoi.
Amma, shin wadannan shugabanni da dukkanin yan Najeriya sun damu da tambayar dalilin da yasa abubuwa ke kara tabarbarewa a kasar da ke cikin addua a kullun?
Amsar mai sauki ce: Najeriya na fuskantar la’anar Allah. Ayoyi da daman a Al-Qurani mai girma da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da ayoyin injila da dama da koyarwar Almasihu sun goyi bayan wannan hasashen.
Alkurani mai girma yana cewa: Ya ku mutane! La’anar Allah ta tabbata a kan wadanda suka aikata ba daidai ba! (Quran 11:18). Littafin Injila ya ce, Laananne ne duk wanda ba ya kiyaye dukan abin da aka rubuta a littafi mai tsarki, ya aikata su.
Har ila yau, Alkurani mai girma yana cewa: Lallai Allah ba zai canza halin da mutane suke ciki ba matukar ba su canza yanayinsu harkokinsu da kansu ba. (Kuran 13:11).

