Site icon Muryar 'Yanci

Najeriya Ce Ta Uku A Duniya ?angaren Rashin Tsaro – Hukumar ?ididdiga

Najeriya ta zo a mataki na uku a jerin kasashen da ta’addancin ya yi wa katutu a fadin duniya, kamar yadda rahoton ?ungiyar ?ididdigar ta’addanci ta duniya (GTI) ta bayyana.

Rahoton ya bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon yakin Boko Haram ya nunka daga shekarar 2018 zuwa 2019, zubar da jinin jama’a ya yawalta sosai.

?asar Afghanistan ce a mataki na farko, sai kuma kasar Iraq a mataki na biyu, a jerin kasashen da ta’addanci ya shahara Najeriya ta na mataki na uku, wato tana kafa?a da kafa?a da wa?ancan ?asashen.

Rahoton da ?ungiyar ta fitar ya nuna cewa adadin yawan mace-mace sanadiyyar ayyukan ?ungiyar Boko Haram ya ?aru da kaso 25% daga shekarar 2018 zuwa 2019, fargaba da tashin hankali ya hauhawa a zu?atan ‘yan Najeriya.

Rahoton ya bada misali da harin da aka kaiwa masu jana’izar gawa a garin Badu Jihar Borno a shekarar 2019 wanda ya kasance mafi muni cikin hare haren ?ungiyar Boko Haram.

?ungiyar GTI ta gano cewar, sanadiyyar ?aruwar masu mace-mace daga hare haren ?ungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas ?in ?asar, Najeriya itace ?asa ta biyu da ta samu hauhawar adadin mace mace sanadiyyar ta’addanci da hargitsi.

“Rahoton ya ce an kashe mutane 2,043 sanadiyyar ayyukan ta’addanci mabambanta a shekarar, amma guda 1,245 kacal aka shigar a rubuce a shekarar 2019.”
A jumullance,mace mace sanadiyyar ta’addanci a duniya ya ragu da kaso 15.5% daga shekarar 2018 zuwa 2019.

“Mace mace daga ta’addanci a Najeriya yanzu haka ya kai kaso 83%, ?asa da adadin shekarar 2014 wanda shine mafi yawa da aka samu a tarihin ?asar, sun ?ara da cewa har yanzu Najeriya na cikin ha?ari sakamakon sabunta ayyukan a ta’addanci da ?ungiyar Boko Haram ta yi a ?asar da ma?wabtanta irinsu Nijar,Kamaru,da Chadi,wanda yin hakan ya zamewa yankin babbar barazana.

“A shekarar 2019, Boko Haram ta aiwatar da hare-haren ?unar ba?in wake guda 11 wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 68, hare haren ?unar ba?in wake suna da kaso 6% cikin mace mace sanadiyyar ayyukan ta’addancin Boko haram a shekarar 2019.

Exit mobile version