Ministan harkokin noma da cigaban karkara, Muhammad Sabo Nanono ya bayyana cewa akwai abubuwan da za su sa kasar ta yi murna da zuwan rana irin ta yau, 1 ga watan Oktoba, wato ranar bikin ‘yancin kai duk da irin kalubalen da ake fuskanta a Najeriya, nasarorin da aka samu a Najeriya sun cancanci ayi murna.
Ina yi maku murna yan Najeriya na cika shekaru 60 da samun yanci a kasarmu. Murnar samun yancin-kai abu ne da ya kamata ayi farin-ciki.
Ministan harkar noman ya kara da cewa dole ayi laakari da nasarorin da aka samu duk da tulin kalubale da ?asar ke fama da su.
A shekarar 2019, Najeriya ta kasance kasar da ta fi kowace kasa noman shinkafa a Nahiyar Afrika, ta doke kasar Masar a karon farko a tarihi. Inji Sabo Nanono.
Ministan ya kara da cewa: Wadannan nasarorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na farfa?o da shaanin noma.
Mu na bukatar hadin-kai tsakanin gwamnati da manoma domin a inganta kokarinmu. Najeriya ta na da karfin da za ta ciyar da kasar nan da makwabta.
Jawabin ministan ya fito ne a shafinsa na Tuwita, @NanonoSabo, a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2020.

