Site icon Muryar 'Yanci

Na Karya Darajar Naira Ne Domin Kubutar Da Najeriya Daga Matsi – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kare kan shi daga zargin masu zargi a game da daidaita farashin kudin kasashen waje da gwamnatinsa ta yi wanda ya karya darajar Naira.

Shugaban kasar ya na wannan bayani ne a wajen bikin da gwamnatin jihar Legas ta shirya domin karrama shi a Marina. Bola Ahmed Tinubu yake cewa ya dauki wannan mataki ne saboda kishin kasa, ya ce idan da ya so zai bari a cigaba da tafiya kan yadda aka saba.

Shugaba Bola Tinubu ya ce zai fi amfana da tsarin da ya soke ta hanyar yin kudi da kasuwar canji, amma ya zabi ya ceto tattalin arzikin Najeriya.

Da yake bayani a wajen taron Tinubu ya kamanta daidaita kudin kasashen ketare da cire tsarin tallafin man fetur da ya yi a baya a matsayin kishin kasa.
“Zan iya amfana da moriyar ta hanyar shiga cikin badakalar, amma Allah ya tsare ni da haka! Ba abin da ya sa ku ka zabe ni ba kenan.

Dole mu dauki wadannan matakan domin kawo karshen matsalar tattalin arzikinmu ta daukar gaggawan mataki kan tallafin man fetur.

Shugaban ya ce zai dage wajen ganin ana amfana da dukiyar da ke kasar, ya kuma nemi goyon bayan Gwamnonin jihohi wajen kawo cigaba a Najeriya, ya ce akwai bukatar hadin-kai wajen bunkasa tattalin arziki.

Exit mobile version