Bayan salati ga Annabi Muhammad (SAW), Muhammadu Sanusi II ya yi ta ambatar InnalilLahi wa inna ilaihi rajiun domin jimamin rashin Alhaji Bashir Tofa.
Mai martaba Sanusi II yace shi karon kan shi ya yi rashin babban masoyi wanda shi da mahaifinsa suka kaunace shi da mahaifinsa da kakansa, Sanusi I.
Ina yi mana gaba daya taaziyyar rashin Alhaji Bashir Othman Tofa, wannan rashi ne ga kasarmu baki daya. Rashi ne ga Kano wanda ta rasa shugaba, jagora wanda zai tsaya a kan martabarta, mutuncinta da kare martabar alummarta da dukiyarta.
Ni kai na wannan rashi ne gare ni babba na masoyi wanda da shi da mahaifinsa, suka nuna kauna da soyayya da Sarki Khalifa (Muhammadu Sanusi) da Ciroma da Dan’ Iya da zuriarmu baki daya. Wannan rashi da jimami duka a mu. Mu na rokon Allah (SWT) ya gafarta masa. Allah ya sa ayyukansa na alheri su bi shi, Allah ya yafe masa kura-kurensa.”
Sanusi II ya ba iyalin Marigayin hakuri, tare da kira ga mutane su cigaba da yi masa adduar gamawa da Duniya lafiya. A karshe Muhammadu Sanusi II ya yi addua Allah ya jikan mu idan lokacin mutuwarmu ya zo.

