Hamsha?in Attajiri ?an kasuwar nan na jihar Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya bayyana cewa a halin da ya ke ciki baya jin da?in rayuwa.
Dantata, mai shekaru 91 a duniya, ya kuma ce shi babban burinsa shi ne ya cika da imani.
Dantata ya bayyana haka ne a jiya Talata yayin da ya kar?i ba?uncin mataimakin ?an takarar mataimakin shugabancin ?asa a jamiyyar APC, Kassim Shettima a gidansa da ke unguwar Koki a jihar Kano.
Ya ce a lokacin ?uryciyarsa ya yi muamala da harkar kasuwanci da mutane masu yawan gaske wanda a yanzu abu ne mai wahala ya zayyano mutum goma da su ke raye.
Na yi yawon fatauci a dukkanin jihohin Najeriya inda na yi muamala da mutane da mafi yawansu abokan cinikayyata ne a wa?annan jihohi. Sai dai abin takaici shi ne a cikin jerin wa?anda mu ka ha?u abu ne mai wahala in zayyano mutum goma da su ke da rai
Maganar gaskiya a halin yanzu ina jiran waadi ne domin bana jin da?in rayuwa, burina in cika da kyau da imani In ji Aminu Dantata.
Haka kuma hamsha?in attajirin ya ?ara da cewa yana fatan duk wanda ya ?ata wa ya yafe masa shi kuma duk wanda ya yi masa ba daidai ba ya yafe masa.

