Labarin dake shigo mana daga Jihar Enugu na bayyana cewar Likitoci a asibitin East Side a Jihar Enugu sun tabbatar da mutuwar jarumar fina-fina ta Nollywood, Chinedu Bernard.
Ta yanke jiki ta fadi ne a yayin da ta ke aikin tsaftace coci na St. Leo the Great Catholic Church da ke rukunin gidajen Tarayya a jihar.
Faston cocin, Rabaran Fada Uchendu Chukwuma, da wasu masu ibada a cocin, sun garzaya da ita asibitin a inda aka tabbatar ta rasu.
A cewar wani rubutu da daya daga cikin masu aiki a cocin ya wallafa, ana kokarin tuntubar yan uwanta kafin a kai gawarta dakin ajiye gawa a asibiti.
Shugaban kungiyar jaruman fina-finai, AGN, ya yi ta’aziyya mai ratsa jiki game da mutuwar Chinedu Benard da wata jarumar Chima Precious. Emeka ya ce yana daf da magana a kan auren mata biyu da jarumi Yul Edochie ya yi ne sai ya samu labarin rasuwar jaruman biyu.
Ya wallafa ta’azziyar a shafinsa na Instagram kuma ya bukaci al’umma su saka su a addu’a.

