Jamiyyar adawa ta PDP a Jihar Kaduna ta lashe akwatin da Gwamnan Jihar, Nasir El-rufai ya kada kuriarsa yayin zaben Kananan Hukumomin Jihar na ranar Asabar.
Sakamakon, wanda Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna Mai Zaman Kanta (KADSIECOM) ta fitar a akwatun mai lamba 001 a Unguwar Sarki da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ya nuna cewa ta sami kuria 86 daga cikin 159 da aka jefa a zaben Shugaban Karamar Hukumar.
A nata bangaren, jamiyyar APC mai mulki kuwa ta sami kuria 62 ne, yayin da APP ta sami daya, ZLP ta sami biyar, PRP hudu.
Kazalika, PDP ta kuma sami kuria 100 daga cikin 162 da aka kada a zaben Kansila, yayin da APC ta sami 53, ZLP biyu, PRP ma biyu, NNPP daya sai kuma BP mai kuria hudu.
Jamiin akwatin, Muhammad Sani ne ya sanar da sakamakon zaben.
Tun da farko dai Gwamnan El-rufai ya shaida wa yan jarida bayan kada kuriarsa cewa ya kirkiro da tsarin zabe da naura mai kwakwalwa ne saboda jamaa su zabi abin da suke so.

