Site icon Muryar 'Yanci

Muna Ciyar Da Yara Miliyan 10 A Kowace Rana – Ministar Jin ?ai

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta samu nasarar ciyar da daliban makaranta milyan goma karkashin shirin ciyar da yan makaranta a fadin tarayya watau NHGSFP.

Ministar tallafi walwala da jin dadin jama’a, Hajya Sadiya Umar Farouq, ta sanar da hakan a Abuja a bikin kaddamar da shirin rabon kayayyakin girki a Abuja.

A cewar Minista Sadiya, gwamnatin tarayya ta dauki masu girki sama da 100,000 aiki don yiwa daliban abinci.

Tace: “A yau, mun zo nan don cika alkawarin shugaban kasa na mikawa hukumomin Abuja kayayyakin girki domin amfanin daliban makaranta dake shirin ciyar da yara.”

“Manufar wannan shiri shine janyo hankalin yara su fara zuwa makaranta, habaka kiwon lafiyarsu ta abinci mai kyau, inganta aikin noma, da kuma samawa miliyoyin mutan karkara ayyukan yi.”

“Saboda haka, ina farin cikin fada muku cewa kawo yanzu, mun samu ciyar da dalibai kimanin milyan 10, mun dauki masu girki 100,000 aiki,” Ta kara.

“Hakazalika muna samar da ayyukan yi da dama irinsu sufuri, aikin noma, da kwanukan zuba abinci.”

Hajiya Sadiya ta ce shirin ciyar da dalibai na cikin kokarin da gwamnatin Buhari keyi wajen fitar da yan Najeriya milyan 100 daga cikin talauci cikin shekaru 10.

Exit mobile version