?ungiyar dattawan Arewacin Naeriya (NEF), ta ce shugaba Muhammadu Buhari abin takaici ne ga arewa.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna ranar Asabar, mai magana da yawun ?ungiyar Hakem Baba-Ahmed ya ce Buhari ya yi alkawarin tabbatar da tsaro da kuma bunkasa tattalin arzikin amma ya kasa yin hakan.
Ya shawarci ?an Arewa su za?i cancanta a za?en 2023.
An gaya wa yan Arewa cewa idan Buhari ya zama shugaban ?asa zai shawo kan matsalolinsu amma komai ya sake ta?ar?arewa a ?ar?ashin mulkina, wannan ba farfaganda ba ce; ba almara ba ce, abu ne a zahiri” in ji shi..
Ya ?ara da cewa Akwai miliyoyin ?an gudun hijira a yankin arewa inda Buhari ya fito sakamakon munanan ayyukan ?an bindiga, amma gwamnati ta ?i amincewa da hakan, wannan ba ita ce Najeriyar da muka za?a a ?ar?ashin Shugaba Buhari ba.

