Hukumar EFCC mai ya?i da cin hanci da rashawa a ta ce ta yi nasara a shari’o’i 3,328 da ta gurfanar da mutanen da take zargi da cin hanci cikin wata 11 na shekarar 2022.
Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa ya zuwa 18 ga watan Nuwamba 2022, sun yi nasarar ?wace ku?i naira miliyan 755 daga hannun tsohon babban akanta na ?asa wa?anda suka mayar wa gwamnati.
Kazalika, EFCC ta ?wace kadarorin alfarma uku daga hannun Kanar Bello Fadile (mai ritaya) – tsohon mataimaki na musamman ga tsohon mai ba shugaban ?asa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki.
