Site icon Muryar 'Yanci

Mun Mallaki Makamin Kare Dangi Domin Kawar Da ‘Yan Ta’adda – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar nan ta samu sabbin makamai da za ta iya yakar kowanne nau’in rashin tsaro, ta kawar da ‘yan ta’adda ta shafe tarihin su gaba ?aya.

Buhari ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin bikin yaye daliban aji na 68 da suka hada da hafsoshin sojin kasa, ruwa da na sama da aka yi a makarantar horar da hafsoshin soji ta NDA da ke Kaduna.

Shugaban kasan ya bayyana damuwarsa kan rashin tsaro inda ya ce ya sakankance cewa sabbin kayan aiki da aka kawo za su matukar taka rawa wurin inganta tsaro a kasar nan, ta inda kasar za ta koma bisa kyakkyawar turba.

“Kamar yadda ku ka sani, kasar Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro a wannan lokacin. Muna cigaba da fuskantar barazana da tashin-tashina ta bangaryne ta’addanci, ‘yan fashin daji, garkuwa da mutane da kashe-kashen da ‘yan siyasa suke sa wa wanda ya ke barazana ga hadin kan kasar nan.”

“Ina tabbatar muku da cewa wannan mulkin zai cigaba da yin duk abinda ya dace wurin dabba’a doka tare da kawar da duk wan nau’i na rikici da ke samar da tsoro da tashin hankali a zukatan ‘yan kasar nan.

“Akwai matukar amfani in sanar da ku cewa mun samu sabbin makaman yakar kowanne rashin tsaro daga kasar nan. Wadannan kadarorin za a tura su wurare daban-daban domin yakar rashin tsaro a dukkan sassan kasar nan.”

Exit mobile version