Site icon Muryar 'Yanci

Mun Fitar Da ‘Yan Najeriya Miliyan 10.5 Daga Talauci – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cire kimanin mutane miliyan 10.5 daga kangin talauci a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ya bayyana hakan ne a safiyar yau a jawabin da ya gabatar a duk fadin kasar don zagayowar Ranar Dimokiradiyya ta bana.

Shugaban ya kuma bayyana tabbacin cewa burin da ake da shi na tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci ya kai ga cin nasara.

Shugaban ya kuma sake nanata kudurinsa na samar da yanayi mai kyau don samar da ingantaccen tsarin zabe a lokacin mulkinsa.

Sannan, ya nuna cewa ana bukatan ‘yan Najeriya su bayar da tasu gudummawar ta hanyar shiga kowane mataki don tallafawa tsarin dimokiradiyya domin yi wa kowa hidima ba wai ga wani bangare ba ko kuma ga wasu’ yan kalilan ba sannan su nemi amana daga shugabannin da suka zaba.

Exit mobile version