Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta du?ufa kan ?o?arin magance tsadar farashin abinci a ?asar.
Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake bu?e taron bita kan ayyukan ministocinsa karo na uku don tantance irin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da ?udurorin da gwamnatinsa ke bai wa fifiko.
Muna yin gagarumin ?o?ari don warware matsalar tashin farashin abinci mai ala?a da hauhawar farashin da ake fama da shi a fa?in duniya.
Al?aluman baya-bayan nan, in ji shi daga Hukumar ?ididdiga ta Najeriya sun nuna cewa hauhawar farashin ?asar ta kai kashi 20.77 a watan Satumba.
Hukumar ta ce hauhawar farashin abiinci ya ?aru ne sakamakon ?aruwar farashin burodi da hatsi da sauran kayan abinci irinsu dankalin turawa da doya da man girki.
A yayin taron, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan raya ?asa masu gagarumin tasiri a fa?in ?asar, don haka shugabancinsa ya cimma muradai da burukan ‘yan Najeriya.
Ya nanata irin ci gaban da aka samu a fannoni kamar aikin gona da tattalin arzi?i da samar da ababen more rayuwa da tsaro da kula da lafiya da ya?i da cin hanci da rashawa.

