Site icon Muryar 'Yanci

Mun Bankado Makudan Kudade Da Kayayyakin Sojoji A Gidan Tukur Mamu – DSS

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Hukumar DSS ta bayyana cewa ta bankado abubuwa da dama a gidan mutumin dake cinikin kudaden fansan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da yan bindiga suka sace wato Tukur Mamu.

Daga cikin abubuwan da suka gano akwai kayan Sojoji, makudan kudaden kasashe daban-daban da sauran wasu muhimman abubuwa.

Kakakin Hukumar, Peter Afunanya, ya bayyana hakan jim ka?an bayan kammala binciken kwa-kwaf da Jami’an hukumar suka yi a gidan Tukur Mamu dake Kaduna.

Afunanya yace abubuwan da suka bankado na da ban tsoron gaske kuma zasu gurfanar da shi a kotu domin girbar abin da ya shuka.

“Kawo yanzu jami’an tsaro sun aiwatar da bincike cikin gida da ofishin Mamu. An gano abubuwan laifi wanda ya hada da kayan Sojoji. “Hakazalika an gano makudan kudaden kasashe daban-daban da na’urorin kasuwanci. Yayinda muke cigaba da yin bincike, ko shakla babu Mamu zai gurfana a kotu.”

Exit mobile version