Kungiyar Tsofaffin Daliban Jamiar Tarayya ta Fasaha da ke Owerri, FUTO, ta ce bai dace hukumar makarantar ta ba Isa Ali Pantami farfesa a jamiar ba, ko ka?an saboda rashin cancanta.
Kungiyar ta bayyana wannan raayin nata ne ta wata takarda wacce sakataren kungiyar na tarayya, Mr Kingsley Azuaru da shugaban kungiyar, Ndubuisi Chijioke, suka sanya hannu.
Dama tun farko kungiyar malaman jamia, ASUU ta bayyana rashin dacewar FUTO ta ba shi matsayin farfesa inda ta shawarce ta da ta kara dubawa.
Kungiyar ta tsame kanta daga cikin masu shirya liyafar karrama Pantami Kamar yadda takardar ta zo: Kungiyar tsofaffin daliban FUTO ta tsaya a matsayin ta na batun rashin dacewar ba Pantami farfesa. Kungiyar ta amince da matsayar ASUU da ta nuna rashin dacewar lamarin kuma NEC ma bata aminta da batun farfesancin Pantami ba.
Sakataren kungiyar na tarayya ya tabbatar da yadda kungiyar ta ke tsaye akan batun rashin dacewar ba Pantami farfesa. Kungiyar ta kara da cewa abin ban takaici ne ace kungiyar dattawan tsofaffin daliban jamiar tana shirin hada liyafa wacce take da niyyar nuna karrama ministan.

