Site icon Muryar 'Yanci

Ministar Ku?i Ta Fallasa Asirin Hauhawar Farashin Kayayyakin Masarufi

Ministar ku?i, kasafi da tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmad, tace hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ta’alla?a ne akan tsadar safara da tafiye tafiye.

“An samu ?arin ku?a?en dako da tafiye tafiye a watanni da suka gabata sakamakon tashin gwauron zabi da man fetur ya yi, wanda shine sinadarin da yawancin ababen hawa da motocin haya ke amfani da shi”.

Zainab ta fadi wannan magana ne lokacin tuntu?ar masana da masu ruwa da tsaki don tattaunawa akan tattalin arzi?i da tsarin kasafin ku?i don tallafawa direbobi daga ma’aikatar ku?i a shekarar 2020.

Ta ce tsarin daftarin dokar zai rage tsadar kudin dako da tafiye tafiye a fa?in ?asar.

Ku?in dako da tafiye tafiye da jama’a suke biya yana ?aruwa da kaso 12.7% duk wata, sannan kuma yana ?aruwa da kaso 48.02% duk shekara.

Wannan shine abin da al?aluman da aka tattara, kamar yadda al?aluman hukumar kididdiga da tattara al?aluma ta ?asa (NBC) suka nuna.

Zainab ta ce dokar ta zo da sabbin tsare tsare ma su ?ayatarwa, ta bada misalin “kasafin ku?i don matafiya” wanda aka tsara shi don tallafawa tare da rage ra?a?in matafiya ta hanyar bibiyar tsarin tafiye-tafiye.

Ministar ta ce “Babban dalilin da yasa mukayi haka, shine mun fahimci tsadar dako da tafiye tafiye na daga cikin jigon abubuwa masu haddasa tsada a tattalin arzi?i.

“Idan ku ka yi duba da yanayin hauhawar farashi, kuma ku ka binciki dalilin hauhawar, za ku ga cewa gundarin dalilin hauhawar farashin ya ta’alla?a akan farashin dako.

“A nan, manufarmu itace mu rage ku?in dako da tafiye tafiye domin sau?a?a kasuwanci don farashin kaya ya ragu gun masu siye.”

Yanayin hauhawar farashin kayayyaki a ?asa ya ?aru zuwa kaso 13.71% a watan Satumba daga kaso 13.22 a watan baya, a ?iddidigar NBS.

Masu hasashe daga FDCL (Financial Derivatives Company Limited) sun ce an kimanta hauhawar farashin kayyaki da kaso 14.5 a watan Oktoba daga kaso 13.7 a watan Satumba.

“Hakan na nufin hauhawar farashin zai kai kimanin watanni 14. Zai kuma kai ?ololuwar mataki a watanni 33.

“Kayan abinci sune za su fi komai hauhawa inda akayi ?iyasin zasu hau da kaso 17.05. Sauran kayayyakin amfani suma ana tsammanin zasu iya kaiwa haka,” a cewarsu.

Gwamnan Babban bankin ?asa, Mr Godwin Emefiele, ya yi magana, kwanan nan, a kan cewar hauhawar farashin kayayyaki da kuma ?ankancewar tattalin arzi?i ya janyo han?oron yin sabbin tsare-tsare da kuma bu?atar ?arfafa sarrafa kayyaki don bun?asar tattalin arzi?i.

Ita kuwa Ministar harkokin jin?ai da walwalar jama’a, Sadiya Farouq, i?irari ta yi cewa basu kar?i sisin wani daga ciki ko wajen Najeriya a matsayin tallafin ya?i da annobar cutar COVID-19 ba.

Exit mobile version