Ministan yada labarai na Alhaji Lai Muhammad ya caccaki Twitter tare da zargin kamfanin da zama mai fuska biyu.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Alhaji Lai ya ce, ya yi wannan zargin ne biyo bayan zanga-zangar masu manyan motoci da ke faruwa a Canada saboda dokar hana zirga-zirga da aka sanya dalilin annobar korona, wanda hakan ya kawo tsaikon kasuwanci da Amurka.
Masu zanga-zangar sun toshe manyan titunan birnin Ontario, wanda hakan ya janyo bacin rai ga kamfanoni da kuma daidaikun mutane har ma da gwamnati.
Gwamnatin kasar ta bayyanasu a matsayin ” ‘yan ta’adda ko kuma wadanda suke rikici da gwamnati”.
Kamfanin asusun da ke tara kudi ya rufe asusun masu zanga-zangar bayan sun tara dala miliyan 10, haka shi ma Twitter ya dakatar da shafinsu yayin da gwamnatin Ontario ta kulle asusunsu mai dauke da miliyoyin kudi da suka tara a intanet.
Sai dai duk ya fa?i wadannan hujjoji ne domin tuna baya lokacin zanga-zangar EndSars, da kasancewar Canada a matsayin daya daga cikin kasashen da suka nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar.#
Da kuma matakin da Twitter ya dauka ya dauka na goge sakon shugaba Buhari da taimaka musu wajen tattara kudade da za a yi amfani da su.

