Ofishin Babban Mai Binciken Ku?a?e na gwamnatin Tarayya ya fallasa yadda aka karkatar da naira miliyan 113.2 a Maaikatar Sharia a cikin 2019.
Ofishin ministan Shari’a ya ce an ?ebi ku?a?en ne aka ce an biya wasu ayyuka da su, amma tsarin biyan ku?in ya kauce wa dokar Kashe Ku?a?en Gwamnantin Tarayya.
An zare ku?a?en an biya ne ta hanyoyi daban-daban da su ka ha?a da biyan yan kwangila tare da shirya bocar biyan ku?a?e da sauran hanyoyin da ba su dace ba.
Tashin farko aka sa?a?a aka waske da wata naira miliyan 35.8. Amma dabarar da aka yi, sai aka karkasa ta gida 12, a cikin 2019, aka yi wa maaikata 12 watandar ku?a?en.

