Sulhu tabbataccan abu ne a cikin Alkur’ani mai girma da Sunnah da ijmain malamai
Yin sulhu yazo kashi biyar a cikin Littafin Allah
- Sulhu tsakanin ma’aurata, Allah ta’ala yace :
?????? ???????? ??????? ??????????? ???????????? ??????? ????? ????????? ????????? ????? ?????????? ??? ????????? ?????????? ????????? ??????? ????????????? ????? ??????? ????? ???????? ????????
Kuma idan kun ji tsõron sã?ãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma’auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa. - Sulhu tsakanin musulmi da suka sami sa?ani da ?arkewar rikici, na addini ko siyasa ko ?abilanci, a ?ai?aiku ko jama’a ko ?asashe. Allah ta’ala yace :
????? ????????????? ???? ?????????????? ???????????? ????????????? ???????????? ?????? ?????? ????????????? ????? ??????????? ???????????? ??????? ??????? ??????? ???????? ??????? ?????? ???????? ????? ???????? ????????????? ??????????? ??????????? ??????????????? ????? ??????? ??????? ????????
Kuma idan jama’a biyu ta m?minai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ?ayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yã?i wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita. Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa.
-Surah Al-Hujurat, Ayah 9
-3. Sulhu tsakanin musulmi da kafurai, wa?anda suke ya?ar mu, sai a ?ulla yarjejeniya, zaman lafiya da fahimtar juna bisa wasu ?aidojin zamantakewa. Allah ta’ala yace:
????? ????????? ?????????? ????????? ????? ??????????? ????? ???????? ???????? ???? ?????????? ??????????
Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Sh?, Mai ji ne Masani.
-Surah Al-Anfal, Ayah 61. - Sulhu tsakanin tsakanin makota, da ?an’uwa, da dangi. Allah ta’ala yace :
?????????????? ???? ???????????? ???? ??????????? ??????? ????????????? ??????????? ??????? ????????????? ????? ??????????? ???????????? ??????? ????????????? ??? ?????? ????????????
Suna tambayar ka ga gan?ma. ka ce: Gan?ma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da ta?awa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ?ã’a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance m?minai.
- Sulhu tsakanin masu hul?a da juna ta ku?i ko kasuwanci ko bashi, ko ajiya ko aro, ko rance, da sauran hul?o?i da suke faruwa tsakanin jama’a. : Allah ta’ala
???? ?????? ??? ??????? ???? ????????????? ?????? ???? ?????? ?????????? ???? ????????? ???? ?????????? ?????? ????????? ????? ???????? ??????? ??????????? ????????? ??????? ???????? ????????? ??????? ????????
Bãbu wani alh?ri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alh?ri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin n?man yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.
-Surah An-Nisa’, Ayah 114
SULHU A CIKIN SUNNAH,
1,Manzon Allah saw ya kasance yana sulhunta masu rigima, ko rashin fahimtar juna.
2, Manzan Allah saw yace : Sulhu ya halatta tsakanin musulmi, face sulhun da zai halatta haram ko ya haramta halal, Abu Dauda( 3594) Tirmiziy (1352.)
SULHU TSAKANIN MALAMAI.
Dukkan malamai sun ha?u akan yin sulhu tsakanin al’umma ya dace da shari’a. da hankali da al’adu masu kyau na zamantakewa.
HANAFAWA, sunce: ana ?ulla sulhu domin kawar da gardama tsakanin al’umma.
????? ??????? ????? ??? ?????? 8/403
MALIKIYYAH sunce: sulhu shine warware rikici ko kiyaye faruwar sa bisa wani hakki da ake nema. ????? ?????? 530.
SHAFIAWA : sunce sulhu shine ?ulla yarjejeniya domin kawar da husuma.
????? ????? 2/382
HANBALIYYAH sunce : sulhu shine : Shawo kan wata matsala da sulhuntawa tsakanin masu sa?ani.
?????? 4/527
MANUFOFIN YIN SULHU
- Yin sulhu yana tsare addini, ya kawo zaman lafiya. Manzon Allah saw yace, shin bana baku labari ba gamai da wani abu wanda yafi darajar azumi da Sada?a da sallah sai sahabbansa suke ce muna so muji, sai yace sulhunta tsakanin ku, domin lalacewar zamantakewa itace mai aski, (wacce take kawar da zaman lafiya kamar yadda mai aski yake aske suma) Abu Dauda( 4919).
- Yin sulhu yana kawar da gaba da kiyayya wacce take kawo rashin zaman lafiya da yawan gardama da husuma tsakanin al’umma. Manzon Allah saw yace : Duk ranar Litinin da Alhamis ana bu?e kofofin aljanna ana yin gafara ga dukkan musulmi wanda baya shirka face masu gaba da juna za a ce a kyale su har sai sun shirya, Muslim 2565.

