Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a wannan rana ta Alhamis da misalin karfe 7 na sanyin safiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yiwa ‘yan kasa jawabi dangane da halin da ?asa ke ciki.
Bayanin hakan na fitowa ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina a cikin wata sanarwar da ya fitar a daren jiya Laraba.
Adesina ya bayyana cewa, za a yada jawabin shugaban kasan a gidajen talabijin, rediyo da sauran kafafen yada labarai na kasar.
Ya zuwa yanzu dai ba san dalilin da yasa shugaban kasan zai yiwa ‘yan Najeriya jawabi ba a daidai lokacin da ‘yan kasar ke cikin matsi.
Jawabin na shugaban kasa dai na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kuka kan yadda karancin takardun Naira ya shafi rayuwarsa ta yau da kullum.

