Babban Limamin Masallachin Juma’a na Sultan Bello Kaduna Dr. Muhammad Suleman ya yi kira ga jama’ar Musulmi da su sanya Najeriya cikin addu’o’in su a lokacin bukukuwan sallah dake gudana domin fita daga halin matsalar tsaro dake addabar kasar.
Limamin ya yi wannan kiran ne a yayin gabatar da hudubar idin salla karama da ya jagoranta a filin idi na Masallachin Juma’a na Sultan Bello da ke Kaduna.
Imam Muhammad Suleman ya kara da cewar tabbas Najeriya na cikin wani mawuyacin hali na ta?ar?arewar tsaro a wannan lokaci, kuma mafita ga halin da ake ciki shine mutane su koma ga Allah ta hanyar yin addu’o’i domin fita daga halin matsalar da ake ciki.
Dangane da halin kuncin rayuwa da jama’a ke ciki na rashi da tsadar rayuwa Limamin ya yi kira ga jama’ar Musulmi masu hali da su taimakawa talakawa Mabu?ata da abin tasarrufin rayuwa musanman a halin da aka tsinci kai a ciki na wahalar rayuwa.
Imam Muhammad Suleman ya yi kira ga jama’ar Musulmi da su cigaba da bin karantarwar addinin Musulunci bisa ga darussan da suka samu a yayin watan azumin Ramadan da ya gabata, su ?ora akan hakan domin dacewa da rahamar Allah madaukakin sarki.

