Site icon Muryar 'Yanci

Matsalar Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Dakatar Da Sarkin Zurmi

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi daga Sarauta, An dakatar da Sarkin ne a bisa dalilin rashin tsaro dake addabar karamar hukumar ta Zurmi dake jihar Zamfara.

Kuma Gwamnan ya nada kwamintin da zai aiwatar da bincike akansa bisa ga tuhume-tuhumen da ake yi masa akan matsalar rashin tsaron.

Wannan dai shine Sarki na hudu da wannan gwamnati ta dakatar kenan.

Shin kowace nasara aka taba samu game da dakatar da Sarakunan da ake yi bisa zargin su kan matsalar tsaro?

Exit mobile version