Site icon Muryar 'Yanci

Matsalar Tsaro: El Rufa’i Ya Yi Wa Atiku Raddi

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi martani game da shawarar da tsohon mataimakin Shugaban ?asa kuma ?an takarar Shugabancin Kasa na jam’iyyar PDP a za?en 2019 Atiku Abubakar, na kiran da a aika sojoji domin su tsare dalibai a fa?in Najeriya.

Malam Nasir El-Rufai ya soki lamirin da shawarar da aka ba gwamnati, ya ce Najeriya ba ta da karfin da za ta iya kai sojoji zuwa kowace makaranta, kamar yadda Atiku ya bukata.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da akayi dashi, inda aka yi masa tambaya game da lamarin matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.

“Ba mu da isassun jami’an tsaro, ina ganin zai fi kyau muyi amfani da kayan yakinmu wajen maganin miyagun da akasari su ke kungurmin jeji.”

“Sai mun jira sun zo makarantu sun kama ‘ya ‘yanmu? Sojoji nawa za ka baza a makarantu su tsare ‘yan bindiga 200 da za su zo a lokaci daya su kai hari?” “Sojoji nawa gare mu? Jami’ai nawa za su rika aiki a Arewa maso gabas da Arewa maso yamma, nawa za ka kai jihar Kaduna inda mu ke da makarantu sama da 300.” Ba zai yiwu ba.

Wasu su na ganin wannan matsalar rashin tsaro dama ce da za su ci da siyasa, su rika kawo shirman shawarwarin da ba za su kai ko ina ba.” “Ban yarda da wannan ba, miyagun ‘yan bindiga ne, marasa gaskiya ne, wanda mafi yawancinsu su ke jeji, mu gano su, mu je mu yi maganinsu.” Inji El-Rufai.

El Rufa’i ya ?ara da cewa bayan an lallasa mafi yawan ‘yan bindigan, za a iya zama da ragowar da su ka tuba, sai ayi masu afuwa, kamar yadda wasu ke fada.

A jawabin da Atiku Abubakar ya yi wa take da: ‘Privatisation of Refineries and Other Assets: Better Late Than Never’, ya ba gwamnatin kasar wasu shawarwari. Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne a wani dogon bayani da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

Exit mobile version