Site icon Muryar 'Yanci

Matsalar Lantarki Da Mai: Gidajen Talabijin Da Rediyo Za Su Durkushe – Ramalan

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu daga cikin tashoshin ya?a labarai dake yankin Arewa suna shawarwarin rufe kafafen su na Takabi da Rediyo kan tsadar Man gudanarwa (GAS).

Tashoshin suna bukatar Gwamnatin tarayya da ta ?auki mataki muddin ana so su ci gaba da yada labaru da shirye-shirye, ganin yadda Man gudanarwa na (Diesel) ya kai kimanin N720 zuwa 730 a kan ko wace lita guda.

Mamallakin gidan Talabijin na Liberty da Rediyo, Tijjani Ramalan ne ya bayyana hakan da yammacin ranar Litinin a ganawarsa da manema labarai a Abuja madadin tashoshin dake Arewaci.

“Muna shan wahala sosan gaske wajen gudanar da shirye-shiryen mu ta fannin watsa su a duniya, kuma bamu da wata hanya da za mu iya magance hakan, kashi 100 na ayyukan mu da muke gabatarwa a TV da Rediyo da (Gas) muke yi saboda babu wutar lantarki”.

Tijjani Ramalan ya ?ara da cewar akwai matsala a gudanar da kasuwancin namu muna shan wuya sosai kuma indai har gwamnati bata iya yin wani abu ba na ganin an inganta wutar lantarki da kuma rage farashin mai, za mu rufe shirye shiryen mu da sallamar ma’aikata.

Exit mobile version