Site icon Muryar 'Yanci

Matasan Najeriya ‘Yan ?waya Ne – ‘Yar Majalisa

?ar majalisa mai wakiltar maza?ar Amuwo Odofin ta 1 a Jihar Legas, Mojisola Alli-Macaulay ta ce mafi yawancin matasan Najeriya cikakkun mashaya ne dake cikin mayen ?wayoyi a kullum.

Alli-Macaulay ta bayyana hakan ne yayin zaman majalisar jihar Legas da aka yi kan sata da ?arna da ?ata gari suka yi sakamakon zanga-zangar EndSARs.

“Ya kamata hukumar wayar da kai ta ?asa ta du?ufa wurin aiki. Akwai bu?atar mu fara wayar da kan matasan mu.
“Suna bu?atar mutanen da za su rika musu magana lokaci zuwa lokaci. Mafi yawancinsu tatil suke da ?wayoyin a kowane lokaci.
“Su kan tafi dandalin sada zumunta su rika karo da abubuwa daban-daban.

Ina fargabar ba ?ananan yara na waya don tsoron abinda za su gani a dandalin sada zumunta. Abin ya lalace.”

Alli-Macaulay ta ce rashin aikin yi ba dalili ne da zai sa matasa ?arna ba, ta ?ara da cewa ba Najeriya kadai ne babu ayyukan yi ba.

“Na yi karatu a Burtaniya kuma na ga matasa da dama ba su da aikin yi amma ba su zama ?ata gari ba. Me zai sa ba zamu mu warware matsalolin mu da kanmu ba?”

?ar majalisar ta ce dukkan wadanda suka yi karatun digiri na iya rungumar sana’ar hannu a maimakon kukan rashin aikin yi.

Exit mobile version