Site icon Muryar 'Yanci

Mataimaki: Dalilina Na Watsi Da Kowa Da Zabar Shettima – Tinubu

‘Dan Takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana tsohon Gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima a matkowa Da Zabar Shettima – Tinubusayin wanda yafi cancantar zama mataimakin sa a zaben shekara mai zuwa.

Tinubu ya shaidawa taron gabatar da wanda zai mara masa baya cewar rayuwar siyasar Sanata Shettima ta bayyana shi a matsayin wanda ya cika duk maradun da ake bukata wajen ganin Jam’iyyar APC ta samu nasarar zaben shekarar 2023 da kuma zama mataimakin shugaban kasar Najeriya.

‘Dan takarar yace ya kammala shiri domin wannan tafiya kuma yana farin cikin zabin abokin sa kuma ‘dan uwa Sanata Shettima a matsayin abokin tafiya.

Tinubu yace ya karanta rubuce rubuce da korafe korafen da jama’a keyi akan zabin Shettima, kuma a matsayin sa na mai bin tafarkin dimokiradiya da kuma neman ci gaba, ya fahimci matsayin da wasu jama’a suke gabatarwa a kasar kuma yana mutunta su, amma kuma yana da yakinin cewar bai yi kuskure wajen zabo tsohon gwamnan Bornon domin mara masa baya ba

Exit mobile version