Site icon Muryar 'Yanci

Masu Sukar Gwamnatin Buhari Basu Da Kunya – Ministan Yada Labarai

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta bayyana ‘yan adawar da ke sukar Shugaban ?asa Buhari cewa ba su da kunya, kuma a adawa za su ?are.

Ministan Harkokin Ya?a Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

PDP da LP dai sun maida wa Buhari Kakkausan raddi, bayan ya bayyana dalilan da ya ce su ka haifar da fa?uwar masu adawa za?en 2023.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa jam’iyyun adawa sun fa?i za?en 2023 ne saboda ci-da-zuci da hangen-Dala, ba shiga birni ba.

Buhari ya ce wannan ci da zucin jam’iyyu ya bai wa APC ?arfin samun sake yin nasarar kafa mulki ko kuma nasarar za?en 2023.

Buhari ya yi wannan fashin ba?in ne a lokacin da ya kar?i ziyarar Gwamnonin APC, bisa jagorancin Gwamna Atiku Bagudu wanda shi ne Shugaban ?ungiyar Gwamnonin APC.

“Jam”iyyun adawa sun ?ata lokaci su na ta kiran masu goya masu baya daga ?asashen waje cewa za su kayar da APC. Amma sai jam’iyyar mu ta yi masu kwasar-karan-mahaukaciya, ta zubar da su ?asa.

“To yanzu ci-da-zucin su ya kai su ya baro su, maimakon nasara, sai matsalolin su ke ta ?aruwa. Sun kasa bayyana wa masu goyon bayan su daga waje, gamsassun dalili.

A cikin sanarwar da Kakakin Ya?a Labaran Lai, Segun Adeyemi ya fitar a ranar Lahadi, Ministan Ya?a Labarai ya ?ara nanata duk abin da Buhari ya fa?a a kan jam’iyyun siyasa.

Ya ce dukkan su sun fi maida hankali wajen ganin sun yaudari masu goya masu baya daga ?asashen waje, wa?anda su ka tabbatar wa cewa su ne za su yi nasara, ba APC ba.

“Kowa ya san APC ta ci za?e na gaskiya, babu magu?i. Idan aka duba, APC ba ta yi nasara a jihar Shugaba Buhari ba, a lokacin za?en shugaban ?asa. To shi kuma Buhari da ya tsoma baki a za?e a yi ba daidai ba, ya gwammace APC ta fa?i a jihar ta sa.” Cewar Lai.

Ya ce dukkan ‘yan takarar da ke ta kartar ?asa da karakainar zuwa Kotun ?aukaka ?ararrakin Za?e, babu wanda ya samu sakamakon da za’a ce har ya na da bakin yin ?orafi ko ?warin-guiwar zuwa kotu.

Exit mobile version