Site icon Muryar 'Yanci

Masu Kiran Raba Kasa Suna Yi Ne Domin Mulki Ya Koma Kudu – Sanata Adamu

An bayyana cewar masu kira da han?oron raba Najeriya a halin yanzu suna yi ne kurum ba domin komai ba sai domin barazana da tursasa mulki ya koma kudanci a shekarar 2023.

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Sanata a yanzu Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a birnin tarayya Abuja.

“Na yi imani cewa ana fama da rashin tsaro amma kururuwan a raba kasa daga wajen shugabannin Kudu saboda suna yi ne domin ganin ba su cin wata ribar gwamnati.”

“Wani lokaci sai ka rika mamakin ko korafin me su ke yi. Idan ka duba duk wasu manyan kujeru a kasar nan, za ka samu Ibo, Bayarabe da mutanen Neja-Delta.” “Wannan surutun duk saboda neman shugaban kasa ne.”

“Matsalarsu ita ce a kan menene Bahaushe zai hau kujerar shugaban kasa bayan Buhari? Ba na yin wani kame-kame; na tsufa, na kuma san yadda Najeriya ta ke aiki.” Gwamnatin Buhari ta na tafiya da kowa.

Da ‘yan jarida su ka tambayi Abdullahi Adamu a game da zama da masu wadannan kira na a raba Najeriya, sai ya ce sai an yi hattara ka da a fada tarkon masu mugun nufi.

Exit mobile version