Daya daga cikin Dattawa a masanaantar finafinai ta Kannywood wanda su ke suka samar da masanaantar tun kusan shekaru 32 da saka gabata ya bayyana dalilan su na komawa baya su zuba ido duk da cewar yadda a ke gudanar da abubuwa a masanaantar ba sa tafiya daidai.
Malam Shuaibu Yawale, ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Dimukaradiyya, in da ya ke cewa A yadda alamura su ke faruwa, idan aka ce kai ba komai ba ne, sai ka zauna ka zuba ido ka gani. Lokacin da ka zamo komai din sai a nemo ka.
Abin da na ke nufi a nan shi ne, masanaantar ce a yanzu ta koma jari Hujja. Kudi na na saka, saboda haka abin da na ga dama shi zan yi. To kai ana yi maka kallon ba ka da kudi, don haka idan ka yi magana ma, sai a ce bakin ciki ka ke yi. Wannan ce ta sa ka ke ganin alamara sun ja baya, kuma idan ka cika magana sai yaro ya fada maka magana ya ce kudin sa ne, don haka sai muka bar su da mutanen gari. Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa muka koma baya, duk lokacin da aka ga ana bukatar mu to za a nemo mu, domin duk lokacin da suka shawo ta fi karfin su ai suna zuwa su nemo mu saboda sun san ba za su iya kashe Wutar ba sai mu.
Muna fatan dai Allah ya sa su gane domin a samar da gyaran da masanaantar da ta ci gaba.

