Site icon Muryar 'Yanci

Manchester United Ta Kammala Sayen Dan Wasan Borussia Sancho

Dan wasan Ingila Jadon Sancho ya ce zuwansa Manchester United wani “babban burina ne da ya cika” bayan kungiyar ta kammala sayensa kan £73m daga Borussia Dortmund.

Sancho shi ne dan wasan Ingila na biyu mafi tsada a tarihi bayan Harry Maguire da yanzu suke wasa a kungiya daya.

Ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a kungiyar ta United.

“Zan ci gaba da yin godiya ga Dortmund bisa damar da ta ba ni ta murza leda a tawagarta ta manyan ‘yan wasa, ko da yake na dade da sanin cewa zan komo Ingila,” a cewar Sancho mai shekara 21.

“Damar da na samu ta zuwa Manchester United wani babban burina ne da ya cika kuma na zaku na nuna kwazo a Gasar Firimiya.

“Wannan tawaga ce ta matasa masu karsashi kuma na sani cewa tare za mu iya sauyawa zuwa wani abu na musamman da zai kawo ci gaban da ‘yan kallo suke so.”

Ranar 1 ga watan Yuli ne United ta amince da batun farashin Sancho da kuma kwangilar shekara biyar da zabin karin wata 12.

Kammala sayen Sancho da United ta yi ta kawo karshen fafutukar da ta dade tana yi domin ganin ta dauki tsohon dan wasan na Manchester City. A bazarar da ta wuce aka yi tsammanin za ta ayi dan wasan amma hakan bai yiwu ba sakamakon rashin amincewa kan farashinsa.

Sancho ya zura kwallaye 50 sanna ya taimaka aka zura kwallaye 57 a wasanni 137 da ya murza a Dortmund.

Kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya ce Old Trafford za ta bai wa Sancho “damar da yake bukata domin baje basirarsa”.

Exit mobile version