Sojojin da suka ham?arar da Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta sun bayyana aniyarsu ta kafa gwamnatin ri?on ?warya kafin gudanar da sabon za?e a ?asar.
Wannan ya biyo bayan bayyanar shugaban a kafar talabijin, inda ya ce ya sauka daga mu?aminsa.
Sojojin sun yi awon gaba da shi tare da firaministansa daga babban birnin ?asar zuwa wani sansanin soja.
?ungiyar Ha?in Kan Afirka ta AU da Majalisar ?inkin Duniya sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.
Shugabannin rundunar sojojin Mali sun bayar da umarnin rufe iyakokin ?asar tare da sanya dokar hana fita da dare, a cewar wata sanarwa da mataimakin shugaban ma’aikatan sojojin sama na ?asar.
“Daga yau, 19 ga watan Agustan 2020, an rufe dukkanin iyakoki na sama da na ?asa har sai baba ta gani. An saka dokar hana fita daga ?arfe 9:00 na dare zuwa 5:00 na asuba har sai baba ta gani,” in ji Kanar-Manjo Ismaël Wagué a wani jawabin talabijin.

