Site icon Muryar 'Yanci

Majalisar Dokokin Kaduna Ta Zama ‘Yar Amshin Shata – Aminu Adam

An bayyana cewar ko shakka babu a halin da ake ciki yanzu majalisar dokokin Jihar Kaduna ta zama tamkar babu ita duba da yadda ‘yan majalisar suka zamo ‘yan amshin Shata ga Gwamna El Rufa’i.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Honorabul Aminu Adam wani jigo a jam’iyyar PDP ta Jihar Kaduna a yayin ganawarsa da manema labarai a Kaduna.

?an Siyasar ya kara da cewar Majalisar ta gaza kai banten ta bisa ga gaza gudanar da ayyukan da jama’ar Jihar suka zabe ta domin shi, ana ta fuskantar karan tsaye da tauye hakkin jama’a daga Gwamna amma sun yi shiru.

Aminu Adam ya bada misali da ?arin ku?in manyan makarantu da El Rufa’i ya yi ba tare da nuna tausayi ba, sannan ‘yan majalisar kowa ya yi gum saboda jefa su cikin aljihu da ya yi wanda hakan ya nuna ba jama’a suke wakilta ba kawunansu suke wakilta.

Aminu Adam wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar majalisar dokokin Jihar ya sha alwashin samar da sauyi idan ya shiga majalisa.

Exit mobile version