Site icon Muryar 'Yanci

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Kisan Fulanin Nasarawa

Majalisar ?inkin Duniya ta yi tir da harin ranar 24 ga watan Janairu da sojojin Najeriya suka kai kan wasu Fulani makiyaya a Jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.

Harin ya yi sanadiyyar kashe mutum a?alla 40, a cewar MDD.

Mai bai wa MDD shawara ta musamman kan kare kisan ?are-dangi, Alice Nderitu, ita ce ta yi wadai da kisan, tana mai bayyana damuwa game da ?aruwar hare-hare a arewa maso yamma da kuma tsakiyar Najeriyar.

“Irin wannan hare-hare a kan mutane kawai saboda ?abilarsu ka iya ta’azzara rikicin ?abilanci, da shiga ?ungiyoyin ‘yan bindiga, da hare-haren ramuwar gayya, wanda zai dinga ?arewa a kan fararen hula,” in ji ta.

Exit mobile version