Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar dattawan na kokarin magance matsalar da za a iya fuskanta a harkar ilmin boko a dalilin tashin kudin makaranta a jamioi.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce za su iya bakin kokarinsu wajen ganin an hana kudin karatun jamia tashi. Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Alhamis.
Ahmad Lawan ya ce ya zauna da jagororin gamayyar kungiyar dalibai na CNG-SW.
Hadimin shugaban majalisar tarayyan kasar, Ola Awoniyi ya fitar da wannan jawabi a makon nan. Jamiu Aliyu Charanchi shi ne ya jagoranci tawagar the Coalition of Northern Groups Students Wing (CNG-SW) zuwa gaban shugaban majalisar tarayyan.
Lawan ya karbi kukan matasan, musamman ganin yadda ake neman kara kudin karatu a wasu jamioin da ke yankin Arewacin Najeriya a wannan yanayi.
Sanata Lawan ya ce za su yi wani abu a kan lamarin duba da muhimmancin ilmi. Lawan ya yi alkawari ba za su bari a samu matsala wajen karatu ba. Ilmi shi ne jigo da wata alumma ko jamaa za su cigaba.
Kuma duk mutanen da ba su maida hankali a kan ilmi ba, ba za su ga cigaba ba.
Tasirin rashin ba ilmi muhimmanci ba zai misaltu ba, baya ga asarar alumma da za ayi, wasu mutane za su kama layukan da ba su da kyau. Ina ganin cewa a wannan marra, bai kamata ayi karin kudin makaranta ba. Kuma ina ganin dole ne gwamnati ta ba harkar ilmi muhimmanci.”

