Site icon Muryar 'Yanci

Majalisa Ta Amince Da Naira Triliyan 13.5 A Matsayin Kasafin Ku?in 2021

Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kasafin kudin 2021 a zamanta na musamman a yau Litinin.

Majalisar ta amince da naira tiriliyan 5.6 a matsayin kudin ayyukan yau da kullum da tiriliyan 4.1 na manyan ayyuka da tiriliyan 3.3 na biyan bashi.

Kazalika, an ware naira tiriliyan 4.1 a matsayin gudummawar da za a tattara domin gudanar da manyan ayyuka.

Jumilla, majalisa ta amince da kudi naira tiriliyan 13.5, karin biliyan biyar kenan a kan wanda Shugaba Buhari ya gabatar mata a watan Oktoba na tiriliyan 13.

Bayan kammala yi wa kasafin karatu na uku a yau, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya nuna jin dadinsa kan yadda suka amince da kasafin kafin tafiya hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

Exit mobile version