Sanata mai wakiltar maza?ar Borno ta Kudu Sanata Ali Ndume ya ce yafi samun natsuwa da kwanciyar hankali idan yana Maiduguri, babban birnin jihar Borno fiye da idan yana garin Abuja, babban birnin kasar Najeriya, sakamakon ha?akar da tsaro ya samu a jihar Borno.
“Ina zama a Abuja da Maiduguri. Amma matukar ina Maiduguri, ina jin kwanciyar hankali fiye da Abuja saboda wani zai iya buga min kofa kuma ya saka min bindiga. A Maiduguri kuwa babu wannan tsoron.”
“A wajen Maiduguri ne ake samun ‘yan ta’adda kuma dama matsorata ne. Sai dai su yi barna kuma su tsere. A kowacce al’umma, ba a iya hana ta’addanci. A Amurka, an samu inda aka dinga harbi a makaranta.
A nan muna da sanannun ‘yan ta’adda kuma sojoji suna yakarsu.” Sanata Ndume, wanda a kodayaushe yake kira ga gwamnati da ta kara zuba kudi a fannin tsaro, ya ce tsaro yana inganta da jajircewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sanata Ndume ya kwarzanta jarumtar Buhari Sanatan ya kwatanta ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ziyarar karfafa guiwa ga dakarun sojin dake filin daga.
“Shugaban kasan yayi yawon sa’o’i shida – Na gaji. Ya shigo wurin karfe 10 kuma muka duba ayyuka masu yawa har zuwa karfe hudu na yamma kafin ya tafi,” yace yayin kwarzanta jarumtar shugaban kasan.

