Gogaggiyar yar siyasarnan, Hajiya Najaatu Muhammad ta caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ta ce gwamnatin Buhari a baibai ta ke tafiya, Sannan ta bayyana yan arewa a matsayin makwadaita kuma munafukai sanan ga tsoron tsiya.
A wata hirarta da gidan Rediyon RFI Hausa Najaatu ta ce; .Duk Gwamnati a duniya babban aikinta shi ne wannIta kasa kare rayuka da dukiyoyin alumma, ba gwamnatin ba hukuma, ba ta da amfani..
wannan gwamnatin ba ta yi wa alumma amfanin komai ba don ta kasa kare musu dukiyoyinsu da rayukansu.
Hajiya Najaatu wacce maaikaciya ce a maikatar kula alamuran yansanda ta ci gaba da cewa; ba a rasa (masu fada mata gaskiya ba), ko mu muna fada. Yanzu ma fada muke, Rayukan mutumin arewa ya zama ba shi da amfani. Mafi yawan mutanen Arewa munafukai ne, mafi yawansu matsorata ne, mafi yawansu makwadaita ne!
Yan siyasar arewa banda tumasanci da karya da sata ba sa komai. Sun shiga siyasa ne ba don alumma ba sai don su cika aljihunsu. Ana kashe yan arewa kamar kiyashi. Banda a arewa ba inda za a yi wannan a zauna lafiya.
Sannan ta ceGwamnatin Muhammadu Buhari ba ta tausayin alumma, musamman alummar arewa, saboda sun yi shiru. Duk idan ka yi shiru ka yarda ke nan. Kashe mutane shi ne kudi a wurin sojojin Nijeriya, shi ne kudi a wurin yan sandan Nijeriya.

