Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ?asar nan tare da hukunta ‘yan siyasar da ke amfani da addini a matsayin makamin ya?in neman za?e.
Rahotanni sun ambato Gwamnan na wannan maganar ne a ranar Talata a Kaduna lokacin bikin ?addamar da babban ofishin ‘gidauniyar zaman lafiya da ci gaba’ ta mai alfarma sarkin musulmi
El-Rufai ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da malaman addini da su ri?a gudanar da addu’o’in samun ingantaccen za?e da samun zaman lafiya a fadin ?asar.
Ya ce Ina so na yi amfani da wannan damar na yi kira ga shugabanninmu da ke nan, masu girma sarakunan gargajiya da malamanmu da su ci gaba da yi wa ?asarmu addu’o’in samun zaman lafiya da samun ingantaccen za?e, tare da yin addu’ar Allah ya za?a wa ?asarmu shugabannin na-gari da za su ha?a kan ?asar tare da ciyar da ita gaba”
”A matsayina na ?an ?asa, kuma gwamna sannan kuma musulmi bana jin da?in yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da addini da ?abilanci a matsayin makaminsu na ya?in neman za?e”, in ji El-Rufai.
Haka kuma gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ?asar tare da hukunta wa?anda ke ?o?arin amfani da addinin a matsayin makamin ya?in neman zabe.

