Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Uwargidan tsohon Shugaban ?asa na mulkin Soji, Janar Sani Abacha, Hajiya Maryam Abacha ta maka gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin El Rufa’i gaban ?uliya.
Rahotanni sun bayyana cewar Iyalan Marigayi Abacha sun kai El Rufa’i Kotu ne sakamakon kwace wata kadara da gwamnatin tayi a Unguwar Rimi Kaduna.
A cikin wa?anda suka shigar da karar tare da Maryam Abacha akwai babban ?an marigayin, Alhaji Mohammed Sani Abacha da sauran iyalai.
Gwamna Nasiru El Rufa’i dai ya yi ?aurin suna wajen rusau da ?wace filayen mutane a Jihar ta Kaduna lamarin da ya jefa ?inbim jama’a cikin tsaka mai wuya.
Maryam Abacha ta ?auki matakin zuwa Kotun ne domin a tursasa gwamnan ya mayar musu da Kadarorin nasu da ya ?wace tun a zangon mulkinsa na farko.

