Kungiyar Lauyoyin Nijeriya ta fara daukar matakin sharia kan matakin shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsawaita waadin Muhammadu Adamu a matsayin Babban Sifetan Yan sandan Nijeriya.
Kungiyar na neman kotu ta fadi inda kundin tsarin mulki ya ba Buhari damar tsawaita waadin Adamu, bayan lokacin da doka ta dibar masa na shekara 35 a aikin gwamnati ya cika a ranar daya ga watan nan.
Ta ce akwai bukatar gaggawa na dawo da karfin doka a kasar a daidai lokacin da jamian da ke tabbatar da dokar a cikin gwamnati suka kasa tsare hakkinta.
Kungiyar lauyoyin na kan matsayar cewa yanzu haka Adamu bai cikin jerin yan sandan Nijeriya, bayan cikarsa shekara 35 yana aiki, tana mai bayyana kara waadin nasa a matsayin saba kundin tsarin mulki.

